in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya zata samu kudaden shiga masu yawa a fannin raya al'a da da yawon bude ido
2016-04-19 14:14:45 cri
Gwamnatin Najeriya ta fara aiwatar da wasu shirin amfani da fannin yawon shakatawa da na nishadantarwa domin sauye sauye domin kafa wani kamfani da zai samun ar mata dakarin kudaden shiga. a fannin yawon bude ido.

Ministan ma'aikatar yada labarai, raya al'adu da yawon bude ido na kasar Lai Mohammed, yace gwamanatin kasar tana dukafa wajen laluibo hanyoyin da zasu samar mata da kudaden shiga ciki hadda fannin al'adu da habaka fasahohin al'ummun kasar, sabanin baya ga man fetur wanda shine kasar da ke dogaroa da shi kwacokan kansa wajen samun kudaden shiga.

Ministan ya tabbbar da hakan ne a lokacin zantawa da manema labarai a birnin Ikko, yace gwamnatin zata gudanar da taron koli game da raya al'adu a Abuja nan gaba cikin wannan wata domin yin nazari game da nazartar hanyoyin cimma wannan al'amariburi.

Mohammed, yace za'a gayyato dukkan masu ruwa da tsaki a fannin raya al'adu da yawon bude ido domin su bada shawarwari game da yadda za'a inganata hanyoyin samun kudaden shiga a wannan fanni.

Yace Najeriya zata kara samun kudaden shiga ta hanyar gayyato baki 'yan kasasashen waje a lokatun gudanar da bukukuwa shekara shekara na al'adun kasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China