in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakiyar firaministan Sin ta halarci dandalin tattaunawar shugabannin jami'o'in Sin da Masar
2016-03-27 13:23:59 cri
A ran 26 ga watan Maris da yamma, mataimakiyar firaministan majalisar gudanarwa ta kasar Sin Liu Yandong ta halarci bikin kammala dandalin tattaunawar shugabannin jami'o'i na kasashen Sin da Masar a babban birnin kasar Masar, Alkahira, tare da gabatar da jawabi.

A cikin jawabinta, Liu Yandong ta bayyana cewa, shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 60 da kafa dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Masar, ya kamata kasashen biyu su mutunta juna yayin da suke inganta shawarwarin dake tsakaninsu bisa fannoni daban daban, ta yadda za a iya karfafa fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu, da kuma ciyar da mu'amalar al'adu a tsakaninsu gaba yadda ya kamata. Haka kuma, ya kamata kasashen biyu su yi koyi da juna, da kuma karfafa mu'amalar al'adu da al'ummomi a tsakanin kasashen biyu ta hanyoyin da za su dace, a sa'i daya kuma, ya kamata a zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa fannonin koyar da ilmi, kimiyya da fasaha, al'adu, kiwon lafiya, yawon shakatawa da dai sauran harkokin da abin ya shafa, ta yadda za a iya ciyar da bunkasuwar kasashen biyu gaba, tare da cimma moriyar juna.

Kaza lika, ya kamata kasashen biyu su kyautata tsarin yin mu'amala a tsakaninsu, da kuma tsara wasu shirye-shirye na musamman, yayin da suke gudanar da karin dandalin yin mu'amala tsakanin al'ummomin kasashen biyu, bisa tsarin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa da kuma tsarin hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka, ta yadda za a iya habaka mu'amalar al'adu a tsakanin kasashen biyu bisa fannoni daban daban, ta yadda lamarin da zai iya kasance abin koyi ga mu'amalar al'adu a tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Bugu da kari, Liu Yandong ta ce, ana fatan jami'o'in kasashen biyu za su iya ci gaba da zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin dake shafar ba da horaswa, nazari da kuma tallafawa zaman takewar al'umma da dai sauransu, domin bude wani sabon shafi na yin musaya a tsakanin malamai da dalibai, yin shawarwari, da kuma raya harkokin ilmi da dai sauransu, ta yadda za a iya zurfafa mu'amalar al'adu da al'ummomi a tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.

Haka kuma, ya kamata a yi amfani da dabarun inganta dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Masar yadda ya kamata, inda za a iya yin shawarwari kan wasu manyan batutuwa da kuma ba da shawara ga al'ummoni, domin ba da gudummawa kan gina wata sabuwar dangantakar diflomasiyya ta moriyar juna a tsakanin kasashen biyu.

Kaza lika, kafin ta halarci wannan biki, Liu Yandong ta kuma halarci bikin fara gina babban ginin kwalejin Confucius a jami'ar Alkahira tare da ministan ilmin kasar Masar, Ashraf Shehhi, inda ta kuma yanke kyallen dake nuna bude bikin nune-nunen hotuna game da harkokin ba da ilmi a jami'a na kasar Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China