Kantin yana kan titin "Chinatown" dake birnin Johannesburg, gaba daya fadinsa ya kai muraba'in mita dubu daya, ciki hada da sassa guda takwas dake shafar ba da ilmi, fasahar zaman takewar al'umma, adabi da fasaha, yara, fayafayan bidiyo da kaset da sauransu, kimiyya da fasaha da kuma kayayyakin al'adu da dai sauransu, kuma gaba daya akwai littattafai sama da dubu 20 a wannan kanti.
A ranar bude babban kantin din, littattafan da suka hada da "Xi Jinping na hira kan yadda za a iya gudanar da harkokin siyasa" na Turanci, "wasu harkoki game da daular Ming" na Turanci, littattafan da mai karbar lambar yabo ta Nobel a fannin adabi na kasar Sin Moyan ya rubuta da kuma wasu littattafan adabi da ba da ilmi sun janyo hankulan mutane sosai, haka kuma, an sayar da kwallon dara da kuma wasan dara iri na Weiqi da dama dake cikin sashen kayayyakin al'adu da motsa jiki na babban kantin din.
Kamfanin Xinzhi shi ne babban kamfanin kasar Sin da ya wallafa da kuma sayar da littattafai da kuma fayafayan bidiyo da kaset da sauransu, tun shekarar 2011, ya zuwa yanzu, kamfanin ya riga ya kafa wasu manyan kantunan sayar da littattafan Sinanci guda bakwai a kasashen Cambodia, Laos, Malaysia, Myanmar, Sri Lanka, Thailand da kuma Nepal. (Maryam)