Kaza lika, an bayyana a cikin wannan rahoto mai taken "yanayin zuba jari kan makamashi na bola-jari" cewa, a shekarar 2015, jarin da kasashe masu tasowa suka zuba a wannan fanni ya karu da kashi 19 bisa dari, adadin da ya kai dallar Amurka biliyan 156, kuma an sami galibin jari daga cikinsu daga kasar Sin.
Dangane da wannan lamari, wasu masana sun yi nazari cewa, dalilan da suka sa aka fi zuba jari kan harkokin makamashi na bola-jari a kasashe masu tasowa a maimakon kasashe masu ci gaba su ne, babban ci gaba da aka samu a kasar Sin kan yin amfani da makamashi na iska da na rana, da babbar karuwar bukatu na wutar lantarki a kasashe masu saurin bunkasuwar tattalin arziki, da raguwar bunkasuwar tattalin arziki a kasashe masu ci gaba, da kuma raguwar tallafin da kasashen Turai suka samar a wannan fanni da dai sauransu. (Maryam)