Wakilin musamman na kasar Sin a taron sauyin yanayi na MDD da ya gudana a birnin Paris na kasar Faransa Xie Zhenhua ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya yau a nan birnin Beijing.
Mr Xie ya ce, ana gina tashohin nukiliya a wasu wurare da suka dace da ke bakin teku kana ana daga matsayin na'urorin da ke wurin.
Bugu da kari, kasar Sin za ta zabi wasu wurare a babban yankin kasar domin gina tashoshin makamashin nukiliya, amma har yanzu ana tattaunawa game da wuraren da suka dace a gina wadannan tashoshi.
Jami'in ya ce, batun tsaro na daga cikin muhimman batutuwan da ya kamata a yi la'akari da su wajen gina wadannan tashoshi shi ne tsaro, don haka kasar Sin ta himmatu wajen tabbatar da samar da na'urori, da kuma wurin da ya dace. (Ibrahim)