in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNEP: Kasar Sin na da karfin raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba
2015-06-11 10:36:26 cri

Mataimakin babban sakataren MDD kuma darektan hukumar tsara fasalin muhalli ta Majalissar (UNEP) Achim Steiner ya bayyana a jiya Laraba cewa, kasar Sin tana da karfin raya tattalin arzikinta ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma kawar da yanayin hazo cikin sauri.

A yayin da Achim Steiner ya halarci taron neman samun shawarwari daga wajen baki kan kiyaye muhalli da raya kasa da Sin ta shirya a kwanan baya, shi da masana da kwararru a fannin ci gaban muhalli na gida da na waje sun ba da shawara ga shugabannin kasar Sin.

A yayin da yake zantawa da manema labaru, ya ba da shawara kan yadda kasar Sin za ta gaggauta bunkasa tattalin arziki ta hanyar rage yawan iskar Carbon da aka fitar, inda yake ganin cewa, ya kamata kasar Sin ta kara zuba jari da kirkiro sabbin kayayyaki domin kyautata ingancin amfani da makamashi.

Bugu da kari, yayin da ya tabo magana kan batun warware matsalar gurbata iska, Achim Steiner ya ce, ko da yake ba za a warware wannan matsalar da ta addabi kasar Sin har na tsawon fiye da shekaru gomai cikin dare daya ba, amma bisa burin kiyaye muhalli da raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba da kasar Sin ta bayar, ana iya sa ran ganin yadda kasar Sin ta samu babban ci gaba a wannan fanni ta hanyar daukar matakai da suka dace.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China