in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararren kasar Amurka ya ce mai yiwuwa kasar Sin za ta kasance jagora game da kiyaye muhallin halittu
2015-06-06 19:14:27 cri
A yayin taron Whitehead na duniya karo na 10, da dandallin tattaunawa kan batun kiyaye muhallin halittu karo na 9 da har yanzu ake yi a kasar Amurka, wani kwararre na kasar ya nuna yabo sosai ga gwamnatin kasar Sin saboda dora muhimmancin da take yi kan kiyaye muhallin halittu. Yana mai cewa, mai yiwuwa ne Sin za ta kasance jagora a fannoni daban daban game da kiyaye muhalli.

Shahararren masanin a fannin kiyaye muhalli na kasar Amurka, wanda ya dauki nauyin shirya taron John B. Cob, Jr. a jiya Juma'a ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta yi niyyar karfafa kiyaye muhallin halittu, wannan abu ne da gwamnatin kasar Amurka ba ta yi ba. Ya kara da cewa, akwai ayyuka da dama da Sin za ta yi domin cimma burin kiyaye muhalli, za ta kuma gamu da matsaloli da dama, amma duk da haka wannan ita ce hanya da ta fi dacewa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China