A kuma 'yan kwanakin baya, wasu kwararru a fannin kiyaye muhallin duniya sun bayyana cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba sakamakon karfafa aikin kare muhallin halittu da take gudanarwa.
Gabanin wannan muhimmiyar rana, bisa alkaluman da rukunin masu nazari na kasa da kasa dake karkashin shugabancin kwararru daga jami'ar New South Wales ta Australiya ya fitar, bayan ya nazarci bayanai daga wani kumbon bincike cikin shekaru 20 da suka gabata, an ce, a cikin 'yan shekarun nan, yawan itatuwan da aka dasa a duniya ya karu, kuma babban musabbabin hakan shi ne, Sin ta dauki matakan dasa itatuwa cikin shekaru da dama da suka gabata.
Binciken ya nuna cewa daga karshen shekaru 80s na karnin da ya wuce, Sin ta fara gudanar da manufar dasa itatuwa a tsaunuka, kana tana ci gaba da dagewa kan wannan manufa, lamarin da ya sa fadin itatuwan da aka dasa ya yi matukar karuwa.
Direktar kwamitin kiyaye albarkatun kasar na Amurka mai kula da yankin Asiya Barbara Finamore, ta ce, tana farin cikin ganin Sin ta dauki hakikanin matakai na kyautata muhalli, inda tun daga farkon shekarar nan ta bana, ta fara aiwatar da sabuwar dokar kiyaye muhalli, a kuma kwanan baya, ta fidda dokar dake shafar kiyaye ruwa, matakin da ya nuna cewa, Sin ta kama hanyar kiyaye muhalli yadda ya kamata.(Bako)