Bisa labarin da manema labaru suka samu, a gun taron kyautata muhallin kauyuka karo na 2 da aka shirya a birnin Guilin dake kasar Sin a jiya Alhamis 5 ga wata, an ce, nan da shekaru biyar masu zuwa, Sin za ta cimma burin sarrafa sharar da mutane suka fitar a yau da kullum da yawansu ya kai sama da kashi 90 cikin 100 a kauyuka don hana su gurbata muhalli, tare da inganta muhimman ababen more rayuwa na samar da ruwa da iskar gas a wuraren.
Tun daga shekarar 2013, Sin ta gaggauta sarrafa shara a kauyukan kasar. Ya zuwa yanzu wato karshen shekarar 2015, an cimma burin a lardunan Sichuan da Shandong da Jiangsu, da birane Beijing da Shanghai, sauran larduna bakwai kamar su Zhejiang da Guangxi suna yin kokari kuma za su cimma burin nan da shekarar 2016.(Bako)