A jawabinsa, Mr.Ban Ki-moon ya bayyana cewa, dimbin tsarurrukan muhallin halittu a yanzu haka na dab da hadari, don haka, lokaci ya yi da a kawo sauyi ga yanayin da ake ciki.
Ban ya kara da cewa, burin da ake neman cimmawa shi ne a inganta zaman rayuwar dan Adam amma ba tare da gurbata muhalli da kuma kawo matsala ga zuriyoyinmu a bukatunsu game da albarkatu ba. Domin cimma wannan buri, ya zama dole mu kawo sauyi ga yadda ake amfani da albarkatun kasa, sa'an nan a rage yawan makamashi da ruwa da sauran albarkatun da ake amfani da su, tare da rage bata abinci.
A ranar 5 watan Yunin shekarar 1972, MDD ta kira wani taro a birnin Stockholm, babban birnin kasar Sweden, inda aka tattauna batun kiyaye muhallin duniya, taron da ya zama na farko a tarihin dan Adam aka yi nazari a kan harkar kiyaye muhalli a fadin duniya. Mahalarta taron sun ba da shawarar kebe ranar da aka fara taron a matsayin ranar kiyaye muhallin duniya. Bisa ga shawarar, a watan Oktoba na waccan shekara, babban taron MDD karo na 27 ya yanke shawarar kafa hukumar kiyaye muhalli, tare da kebe ranar 5 ga watan Yuni na kowace shekara a matsayin ranar kiyaye muhallin duniya.(Lubabatu)