in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta bullo da shirin rage fitar da iskar da ke dumama yanayi kafin wa'adin da aka tsara
2015-06-09 19:52:53 cri
Wasu rahotanni da cibiyoyin nazarin tattalin arziki dake birnin London suka fitar na bayyana cewa, shirin kasar Sin na rage fitar da iskar gas dake dumama yanayin duniya zai fara aiki kusan shekaru biyar kafin lokacin da aka tsara.

Bugu da kari masu bincike sun bayyana cewa, idan har shirin gwamnatin kasar Sin na rage iskar gas din da ke dumama yanayin duniya ya fara aiki a shekarar 2025 hakan na nuna cewa, za a iya rage dumamar yanayin da duniya ke fuskanta na sama da ma'aunin digrin zafi na Celcius biyu fiye da wanda masana'antu ke fitarwa.

Rahotan ya ce, rawar da Sin ke takawa a wannan fanni zai yi tasiri ga bangaren tattalin azrikin duniya kana ya kara samar da haske ga kokarin da ake na rage fitar da iskar da ke dumama yanayi kamar yadda ake fata.

Taron da MDD za ta kira a Paris game da canjin yanayi a wani lokaci a wannan shekara, zai yi nasara ce idan har gwamnatocin kasashe suka fahimci irin canjin da aka samu a kasar Sin, illolinsa ga dumamar duniya da kuma tasirinsa ga raya masana'antu marasa gurbata muhalli, zuba jari da shirye-shirye da ake niyyar bullowa a kasuwannin duniya game da kayayyaki da hidimomin marasa gurbata muhalli. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China