Shugaban kasar Benin Boni Yayi ya kaddamar a ranar Litinin a Djregbe, birnin dake tazarar kilomita talatin daga kudu maso gabashin birnin Cotonou, da kamfe karo na 31 na ranar dasa itatuwa ta kasa da ke kuma bayyana aiki shuka bishiyoyi a dukkan fadin kasar.
Bisa taken "mu shuka kuma mu kula da itatuwa, ko wace rana, a ko wane biki, domin kasar Benin ta kasance kore", wannan ranar shuka itatuwa ta kasa da kamfen shuka bishiyoyi sun kasance wasu ayyukan sake maido albarkatun dazuzzuka a kasar Benin.
Mayar da kasar Benin kore, bai kasance wani take kawai ba. Wata niyya ce ta yin aiki mai kyau dake shaida hangen makomarmu, in ji ministan muhallin kasar Benin, dake kula da harkar canjin yanayi, da kare albarkatun muhalli, mista Rapheal Edou.
A cewar wannan jami'i dake kula da ma'aikatun kula da muhalli, canjin yanayi ya kasance babban kalubale na wannan zamani.
Tun daga nan, aikin maido da dazuzzuka ya zama wata hanyar yaki da canjin yanayi, in ji mista Edou.
Haka kuma ya cigaba da cewa, a kasar Benin, domin bullo da mafita mai karko ga barazanar sauyin yanayi da kashe itatuwa, gwamnati ta gudanar da sauye sauye da dama, musammun ma karfafa matakan shuka itatuwa ta hanyar aiwatar da "shirin mutane miliyan goma, itatuwa miliyan goma" da ke da manufar kara janyo hankalin ko wane dan kasar Benin wajen dasa itatuwa domin kyautata tsarin zaman rayuwarsu. (Maman Ada)