Babban burin yin kwaskwarima game da wannan fanni shi ne, ya zuwa shekarar 2020, za a kafa wani kammalallan tsarin kiyaye muhallin halittu da ke kunshe da alhakin da za a dauka, wanda zai iya sa kaimi ga raya batun kiyaye muhalli a kasar Sin, ta hakan, gwamnatin za ta iya daidaita batun ta hanyar zamani. Kasar Sin na daukar tsayayyiyar anniya wajen kiyaye muhallin halittu, kuma an gaggauta raya batun a kasar da ba a taba ganin irinsa ba. Kazalika , Sin ta yanke shawarar canja yanayin da kasar ke ciki, wato rashin isassun albarkatu, da gurbatar muhalli, da dai sauransu.
Direktan kwamitin yin kwaskwarima da samun ci gaba na kasar Sin Xu Shaoshi ya ce, kiyaye muhallin halittu ya kasance wata sabuwar manufa da wani sabon salon samun ci gaba, kuma ya zama wani babban aikin da ake gudanarwa, wanda zai iya kawo ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba daga dukkan fannoni a kasar. (Bako)