Masu wallafa takardar bayanin sun hada da masanan jami'ar horar da malamai ta lardin Fujian na kasar Sin, da na cibiyar nazarin fasahar tsara muhalli ta ma'aikatar kare muhallin kasar, da na mujallar kula da duniya ta cibiyar nazarin fasahar samun ci gaba ta majalisar gudanarwar kasar, da dai makamantansu. Wadannan sassa sun yi nazari ne kan yanayin da kasashe 133 suke ciki a kokarin kare muhalli.
Takardar ta sheda cewa, cikin kasashe 30 dake kan gaba a jerin sunayen, 17 daga cikin su kasashe ne masu sukuni, yayin da kuma kusan dukkan kasashen dake koma baya a wannan fanni kasashe ne da tattalin arzikinsu ke tasowa. Dalilin da ya sa haka a cewar takardar, shi ne an dade ana samun babban gibi tsakanin kasashe masu sukuni da kasashe masu tasowa, musamman a fannonin ci gaban tattalin arziki, da yawan kudin da ake zubawa a fannin kare muhalli, da tsarin gudanar da aikin kare muhalli, da ingancin fasahar daidaita muhalli, da dai makamantansu.
Sa'an nan, idan an kwatanta yanayin da ake ciki a nahiyoyi 6 na duniya, za a ga cewa nahiyar Oceania ta fi ci gaba ta fuskar samun ingancin muhalli a shekarar 2014, yayin da nahiyar Afirka ta fi koma baya, a cewar takardar bayanin. (Bello Wang)