A sakon sa na ranar muhalli ta duniya Mr. Ban ya ce, filyen jama'a suna da muhimmanci ga talakawa da wadanda basu da galihu saboda za su iya samar da manyan ababen more rayuwa, su kuma inganta cudanya, raya tattalin arziki da kuma daga darajar gidaje sannan su samar ma yankin kudin shiga.
Mr Ban ya ce, sakamakon amincewa da ajandar samun dauwammen ci gaba a shekara ta 2030 shirin da ya kunshi aniyyar samar da tsaro a birane da wuraren zaman jama'a suna da cigaba kasashen duniya sun cimma ma matsaya da ya amince da cigaba da inganta birane a wani mataki na kawo sauyi.
A don haka Magatakardar na MDD ya ce yana fatan yin aiki da kowa domin ganin al'umma daga ko ina sun amfana da filayen da ke kewaye da su inda kowa yake da matsayi guda, kana kowa ke iya nuna tarihi da al'adunsa, yadda kuma za mu tsara makoma mai samun dawwamammen ci gaba ga kowa a nan gaba.
An kebe wannan rana ce a duk shekara domin fahimtar 'yancin da jama'a ke da shi na samun wurin zama da kuma baiwa hukumomi a matakan karkaka kwarin gwiwar daukan matakan kawar da matsalar karancin gidaje.
A shekarar 1985 ne babban taron MDD ya tsaida ranar a litinin ta farkon watan oktoba ya zama ranar kula da muhalli ta duniya. Kuma teken bikin na bana shi ne filiyan jama'a ga kowa.