Kwamitin sulhun MDD ya ba da sanarwar shugabansa a jiya Ahamis 17 ga wata, inda ya yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki a Sudan ta Kudu, da su aiwatar da yarjejeniyar warware rikicin kasar, domin ingiza yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar.
Sanarwar ta kuma ce kwamitin ya damu matuka da ganin yadda bangarori daban-daban suka ki amincewa da wannan yarjejeniya, ya kuma jaddada kira ga gwamnatin kasar da tsagin 'yan adawa, da su dakatar da bude wuta tsakaninsu, don cimma nasarar matakan tsaron da aka tsayar a baya.
Kwamitin ya kuma nuna rashin jin dadi game da yanayin jin kai da ya kara tsananta a kasar, yana mai kira ga sassan kasar biyu da su ba da dama ga aikin jin kai, ta yadda za a kai dauki ga mutanen da suke da bukata ba tare da gamuwa da matsala ba. (Amina)