Farhan Haq, shine mataimakin jami'i mai Magana da yawun MDD ya ce sakamakon tabarbarewar tsaro ya hana masu kai agajin samun damar shiga yankunan domin kai kayan tallafi, sai dai suna ci gaba da tuntubar bangarorin da abin ya shafa domin samun damar shigar da kayayyakin agaji yankunan.
Haq, ya ce, a halin yanzu suna rarraba muhimman kayayyakin jinkai na amfanin gida ga mutane kusan 17,500 wadanda ke neman daukin gaggawa a yammacin Mundri, daga cikin su har da wadanda suka yi hasarar kayayyakin su, da wadanda wuta ta kone musu kaya.
Ya kara da cewa, a watan Disambar shekarar 2015, an raba kayayyakin jinkai ga mutane dubu 10 a yankin.
Wani rahoto ya bayyana cewer, Sudan ta kudu na cikin mawuyacin hali, inda aka kiyasta mutane sama da miliyan 7 ne ke fama da karancin abinci, da barazanar barkewar cutar Malariya a jaririyar kasar.(Ahmad Fagam)