Harin dai ya auku a wata mafakar da majalisar ta kafa a Malakale, wani muhimmin birni dake arewa maso gabashin Sudan ta Kudu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 18, yayin da wasu 50 suka jikkata, hakan ya sa da kakkausar murya, kwamitin ya yi tir da wannan danyen aikin da aka yi.
Kwamitin kuma ya ce, majalisar ta yi Allah wadai da duk wani matakin da fafutuka suka yi wa fararen hula ko MDD. Ban da wannan kuma, ya yi kira ga bangarori daban-daban masu ruwa da tsaki da su yi hakuri don kauracewar haifar da rikici mai tsanani, sai dai kuma ya kalubanci Sudan ta Kudu da ta yi bincike nan da nan kan lamarin karkashin taimakon da tawagar musamman ta MDD dake Sudan ta Kudu ke bayarwa.
Kakakin babban magatakardan MDD Mista Stephane Dujarric ya nuna a ran 19 ga wata cewa, Mista Ban Ki Moon zai kai ziyarar aiki a Sudan ta Kudu a mako mai zuwa don gana da shugaban kasar Mista Salva Kiir Mayardit, tare kuma da kai ziyara a mafakar da majalisar ta kafa a kasar don baiwa 'yan gudun hijira taimako. (Amina)