Rahoton wanda MDDr ta fitar a jiya Alhamis, ya zargi tsagin dakarun gwamnatin Sudan na SPLA da na 'yan tawayen SPLM/A-IO da nuna karfin tuwo, a ci gaba da dauki ba dadin da suke yi da juna, tun bayan barkewar tashe-tashen hankula shekaru biyun da suka gabata.
Rahoton ya kara da cewa tashe-tashen hankula sun fi tsananta a yankin daga shekarar 2013 kawo yanzu, musamman ma tsakiya da kuma karshen shekarar. Bincike ya nuna cewa cikin yankuna da dama da fadace-fadacen suka shafa, kalilan ne ke cikin yanani na tsaro a yanzu haka, kasancewar wuraren ibada da asibitoci, da ma sansanonin 'yan gudun hijirar MDD, su ma ba su tsira daga hare-haren mayaka ba.
Cikin wata sanarwa da ya fitar game da wannan batu, kwamishina mai lura da harkokin kare hakkin bil adama na MDD Zeid Ra'ad Al Hussein, ya ce yawaitar cin zarafin mata, da bautar da mutane, tare da kisan gilla da ake yiwa jama'ar yanki, da shigar da dubban yara kanana ayyukan soji, tare kuma da raba al'ummar yankin da matsugunan su, abubuwa ne da ya wajaba a gaggauta dakatar da aukuwar su. (Saminu)