Rahoton wanda shirin samar da abinci da aikin gona (FAO) da asusun tallafawa yara na MDD da shirin samar da abinci na duniya (WFP) suka fitar, sun bayyana cewa, akwai kimanin mutane miliyan 2.8, kimanin kashi 25 cikin 100 na yawan al'ummar kasar dake fama da matsalar karancin abinci.
Sanarwar ta ce, wadannan al'ummomin suna bukatar daukin gaggauwa, baya ga wasu mutane a kalla dubu 40 da ka iya mutuwa saboda rashin abin da za su sanya a bakin salati.
Hukumomin sun kuma bayyana cewa, yanzu haka ana shirin shiga lokacin kaka, lamarin da ka iya kara haifar da kunci da mutanen da ke fama da matsalar yunwa.
Don haka, hukumomin suka yi kiran da a hanzarta aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka sanya hannu a shekarar da ta gabata, sannan a yi kokarin kai kayan abinci ga yankunan da ke fama da rikici wadanda ke matukar agaji ba tare da gindaya wani shadari ba. (Ibrahim Yaya)