Wata kafar yada labarai ta kasar Sudan ta Kudu ta bada sanarwa a Talatar nan cewar, fada ya barke tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a Yambio wani birni dake yankin Western Equatoria a Sudan ta Kudu.
Fadan dai ya barke ne tsakanin dakarun gwamnati da'yan tada kayar baya da ke yiwa kansu lakabi da "arrow boys" wadanda suke biyayya ga babbar kungiyar'yan tawayen kasar wadda tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar ke jagoranta.
Sai dai har yanzu babu wani rahoto game da samun hasarar rayuka.
A watan Augusta ne, kungiyoyin da ba sa ga maciji da juna suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya karkashin jagorancin babbar tawaga mai shiga tsakani ta kungiyar cigabn Afrika, sai dai bangarorin biyu na zargin juna da saba yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla.
Sudan ta Kudu ta fada ciki tashin hankali ne, tun a watan Disambar shekarar 2013, yayin da fada ya rincabe tsakanin mayaka dake biyayya ga shugaban kasar Salva Kiir da masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar.(Ahmad Fagam)