Mai Magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya shedawa 'yan jaridu cewar matasa 'yan kabilar Shilluk da Dinka ne suka afkawa junansu inda suka yi amfani da wasu kananan makamai da wukake a daren jiya.
A cewar rahoton binciken farko da UNMISS ta gudanar, an hallaka 'yan gudun hijira 5, yayin da aka jikkata mutane 30 a rikicin.
Dujarric ya ce, fadan ya ci gaba da bazuwa har zuwa wayewar gari, sai dai ofishin MDD ya gargadi al'ummomin da su kai zuciya nesa, kuma su warware duk wata takaddama dake tsakanin su ta hanyar tattaunawa.(Ahmad Fagam)