Hakan ya fito ne a cikin wata sanarawa lokacin da James Wani Igga mataimakin shugaban kasar yake jawabi a taron MDD da ya shiga kwana na hudu a wannan rana.
Ya ce zaman lafiya da tsaro na al'ummar kasar Sudan ta kudu yana gaba da komai wajen gwamnatin kasar bayan da aka kafa ta a shekara ta 2011.
A cikin jawabin nashi, mataimakin shugaban kasar ya ce zai yi amfani da wannan dama wajen kira da 'yan uwa da abokan arziki da kuma magoya bayan kasar Sudan ta Kudu da su gaggauta shiga cikin ayyukan ba da gudunmuwar jin kai, sake farfadowa, samar da zaman lafiya da gina kasa baki daya.
Ya kuma yi nuni da cewa takunkumin da aka kakabawa kasar ya kamata a dage shi.
A cewar James Wani Igga Sudan ta kudu tana da kokari kuma akwai makoma mai haske a gabanta musamman idan aka yi la'akari da dukkan taimako da hadin kai da kasashen duniya ke ba ta. Don haka ya ce bai kamata a ware ta babu dalili ba a kuma kakkaba mata takunkumi ganin cewa jaririyar kasa ce. (Fatimah Jibril)