Haha kuma, bayan ya gana da takwaransa na kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma a birnin Pretoria, mista Kiir ya yi imanin cewa akwai kalubaloli da dama wajen aiwatar da wannan yarjejeniya, amma ya rantse cewa za'a jure su.
Mista Salva Kiir ya yi wannan ziyara kuma domin karfafa huldar dangantaka a fannonin siyasa da tattalin arziki dake tsakanin kasashe biyu, da kuma neman goyon bayan gwamnatin Afrika ta Kudu wajen daidaita rikicin siyasa a Sudan ta Kudu. (Maman Ada)