A ganawar sa da manema labarai, kakakin ya ce tawagar ta kuma samu kaiwa ga makwabtan yankuna kamar su Mundri ta gabas da yammacin yankuna duk dai a jihar yammacin Equatorial domin su yi kididdiga da kuma samar da kayyakin kiwon lafiya da sauran abubuwan da ke bukata.
Tawagar sun yi kiyasin cewa kusan mutane 50,000 ne suka rasa matsuguni da kuma suke bukatar taimakon gaggawa na abincin, ruwan sha da matsugunni a yankunan biyu.
Kakakin majlissar ya ce kaiwa ga mutanen da ke da bukatar taimako a yammacin Equatorial ya zama wani babban kalubale saboda mafi yawansu suna boye ne a cikin daji sun kaurace ma kauyukan su.
Tashin hankali ya barke ne da harbe harbe mai tsanani tun kusan farkon watan Augusta tsakanin kabilu masu dauke da makamai a Yambio babban birnin jihar Yammacin Equatorial na kasar. (Fatimah)