Kalaman na mista Ban sun nuna cewar, duk wani yunkurin tada tarzoma kan fararen hula a harabar da jami'an aikin wanzar da zama lafiya na MDD suke, tamkar aikata laifukan yaki ne.
Mai Magana da yawun Sakatare Janar na MDD Stephane Dujarric, ya fada cewar, Ban ya damu matuka game da zaman tankiya dake wanzuwa tsakanin al'ummar kabilun Dinka da Shilluk.
Ban, ya gargadi alummomin biyu dasu kai zuciya nesa, kuma su guji aikata duk wani abin da ka iya haddasa barkewar tashin hankali a tsakanin su.
Sanarwar ta kara da cewa Ban ya shawarci gwamnati, da jami'an tsaro, da dukkan masu ruwa da tsaki dasu sa ido, domin hana duk wani yunkuri na tada husuma a harabar ofishin MDD.(Ahmad Fagam)