A wata sanarwa ta hadin gwiwa tsakanin wasu hukumomin wato hukumar samar da abinci ta duniya FAO da asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF da shirin samar da abinci na duniya WFP a jiya Alhamis sun tabbatar da cewar matasalar matsananciyar yunwa na neman gigita mutane miliyan 3 da dubu 900 a Sudan ta Kudu.
A wata kididdigar hukumomin, babban darakatan hukumar WFP Joyce Luma, ya ce mutane dubu 300 na rayuwa cikin matsananacin hali na yunwa da barazanar mutuwa a akamakon yunwa a Sudan ta kudun.
Luma, ya ce al'ummar Sudan ta kudun na bukatar daukin gaggawa wajen samar musu da abinci mai gina jiki da magunguna da sauran kayayyakin tallafi domin mayar da komada daga halin da suke ciki.
A nasa bangaren wakilin hukumar UNICEF Jonathan Veitch, ya ce tun bayan barkewar tashin hankali a Sudan ta Kudun, sama da shekaru biyu ke nan, kananan yara a kasar na fama da matsalar cututuka da yunwa da kuma fargaba.
Sanarwar ta ce sakamakon tashin hankalin dake faruwa, an hana jami'an ba da agaji damar shiga yankin kuma matukar ba'a samar da yanayin shigar da kayayyakin tallafi cikin kasar ba to lamarin zai iya cigaba da ta'azzara. (Ahmad)