An kira cikakken taro karo na uku, na taron shekara-shekara na NPC a safiyar yau din nan Lahadi 13 ga wata, don sauraron rahoton kotun koli daga Mista Zhou Qiang, da kuma sauraron rahoton aiki na kotun bincike shari'a daga Mista Cao Jianming.
Rahotanni na cewa kotun kolin ta karbi kararraki 15,985 a shekarar bara, adadin da ya karu da kashi 42.6 cikin dari bisa na shekarar da ta gabace ta. Kana akwai kararraki 14, 135 daga cikin wancan adadi da aka kammala shari'ar su a baran, adadin da ya karu da kashi 43 cikin dari bisa na shekara biyun da suka gabata.
Ban da wannan kuma, yawan batutuwan shari'a da aka kawo karshen shari'ar su, wadanda kuma suka jibanci barazana ga tsaron kasa, da kuma amfani da karfin tuwo ko ta'addanci, sun kai 1,084, inda aka yankewa mutane 1,419 hukunci game da su.
Mista Zhou Qiang ya ce, a shekarar bara an kammala shari'ar wasu manyan laifufuka 15, ciki hadda batun Zhou Yongkang da aka tuhuma da cin hanci da karbar rashawa, tare da amfani da ikon ba bisa ka'ida ba, inda aka tabbatar da cewa ya fallasa bayanan asirin kasar Sin. Har wa yau akwai batun Jiang Jiemin da dai sauransu. Matakan da suka bayyana aniyyar gwamanatin na yaki da cin hanci da sauran miyagun laifuffuka.
Dadin dadawa, an ce, a shekarar bara, kotunan wurare daban-daban sun kawo kammala shari'un mutane dubu 49, masu alaka da cin hanci da karbar rashawa a shari'u dubu 34, ciki hadda manyan jami'ai 134.
Bugu da kari kotunan bincike shari'a na wurare daban daban sun ba da iznin cafke mutane da aka tuhuma da aikata laifuka 873,148, an kuma gurfanar da mutane gaban shari'a sau 1,390,933.
Haka zalika, kotunan binciken shari'a sun gudanar da bincike kan wasu manyan jami'ai 41 ciki hadda Ling Jihua, da Su Rong, aka kuma gurfanar da wasu manyan jami'ai 22, ciki hadda Zhou Yongkang, da Jiang Jiemin da dai sauransu. Yawan mutane da aka bincika game da batun cin hanci ya kai 13,210.
Ban da wannan kuma, kotunan sun aiwatar da bincike kan laifukan cin hanci da karbar rashawa, tare da mayar da kudade da aka tsere da su zuwa kasashen waje.
Tun daga watan Oktomba na shekarar 2014, yawan jami'an da aka tuso keyarsu zuwa nan kasar Sin, wadanda suka aikata laifuka ya kai mutum 124, kuma an cafke 17 daga cikinsu, wadanda ake zargi da aikata manyan laifufuka. (Amina)