Game da wannan dokar dake jawo hankali mutane da dama, Mista Chen ya bayyana cewa, an kafa wannan doka ba wai da burin kara buga haraji ba, amma domin ana son kafa wani tsari mai kyau don rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli.
Har ila yau Mista Chen ya ce, za a saurari ra'ayin bangarori daban-daban don karkata hanyar warware batun muhalli ta buga haraji.
Ban da wannan kuma, Mista Chen ya ce, Sin ta shiga wani sabon yanayi na bunkasa tattalin arzikinta, kuma tana mai da hankali sosai kan samun bunkasuwa mai inganci a dukkan fannoni ciki hadda kiyaye muhalli. (Amina)