Kasar Sin ta ce, ba za ta cire rai na gano jirgin saman nan da ya bace na kasar Malaysiya mai dauke da sinawa 154 ba, muddin tana sa ran cewa, tabbas za'a gan shi,in ji firaministan kasar Li Keqiang.
Mr. Li wanda ya bayyana hakan a wajen taron manema labarai a yau Alhamis bayan rufe manyan taruka biyu na shekara shekara na majalissar dokokin kasar, ya ce, gwamnatin Sin ta bukaci duk wadanda ke gudanar da aikin neman jirgin a yanzu da su kara azama domin taimakawa wajen gano dalilin bacewar jirgin da kuma inda yake cikin lokaci.
Jirgin mai lamba MH370 na dauke da fasinjoji 227 da ma'aikatan jirgin 12 lokacin da ya bace a ranar Asabar 8 ga wata a kan hanyarsa ta zuwa nan birnin Beijing daga Kuala Lumpur bayan da aka kasa jin duriyarsa a sararin teku tsakanin Malaysia da Vietnam. (Fatimah)