Kamar yadda firaministan kasar Sin Li Keqiang ya fada, dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, dangantaka ce a tsakanin wata kasa mai tasowa kuma mafi girma da kuma wata kasa mai sukuni kuma mafi girma. Kasar Sin na son kafa sabuwar hulda irin ta tsakanin manyan kasashe, kamar kasar Amurka da ita, da a cikinta ake bukatar girmama juna, yin hadin gwiwa domin samun nasara tare, hana abkuwar rikici a tsakaninsu, da kawar da kiyayya da junansu.
Firaministan kasar Sin ya fadi hakan ne yau Lahadi 15 ga wata a yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru na gida da na ketare bayan kammala taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, NPC.
Li Keqiang ya kara da cewa, gudanar da harkokinta yadda ya kamata tare da samun ci gaba mai dacewa, da kasar Sin ke kokarin yi, wata babbar gudummowa ce da kasar Sin take bayarwa ga kasashen duniya. Kana kuma kasar Sin tana kara sauke wajababben nauyinta a cikin al'amuran kasa da kasa.
A cewar firaministan kasar Sin, babu shakka akwai sabani a tsakanin Sin da Amurka, yayin da kuma suke samun moriyar bai daya a sassa daban daban. Daidaita sabanin da ke tsakaninsu yadda ya kamata zai iya habaka fannonin da za su inganta moriyar bai daya a tsakanin kasashen 2.
Haka zalika a cewar firaminista Li Keqiang, a cikin wannan shekara, shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai kai ziyarar aiki a Amurka, wanda tabbas ne za a kara azama kan bunkasuwar huldar da ke tsakanin Sin da Amurka. (Tasallah Yuan)