in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi kasashen duniya su hada kai wajen yaki da 'yan ta'adda, a cewar kasar Sin
2015-03-02 19:17:11 cri

Lv Xinhua, kakakin cikakken zama na shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo 12 ya bayyana yau Litinin 2 ga wata cewa, har kullum kasar Sin na tsayawa wajen ganin kasashen duniya sun hada kansu wajen yaki da ta'addanci. A shekarar bara ne kasar Sin ta ba da muhimmanci wajen yaki da kungiyar 'yan ta'adda ta ETIM, inda ta mai da hankali kan yin hadin gwiwa a kasashen dake makwabtaka da ita, kamar kasashen kudanci, gabashi da tsakiyar Asiya wajen yaki da 'yan ta'adda.

A yau da yamma ne aka gudanar da taron manema labau kan cikakken zama na shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo 12 a nan birnin Beijing.

Kakain taron Mista Lv ya fayyace cewa, ya zuwa yanzu kasar Sin da wasu kasashe fiye da 10 sun kafa tsarin yin hadin gwiwa a tsakaninsu wajen yaki da ta'addanci, sa'an nan ta shiga tsare-tsaren yin hadin gwiwa da bangarori daban daban, kamar MDD, kungiyar hadin gwiwar Shanghai wato SCO, taron dandalin tattaunawar kasa da kasa kan yaki da ta'addanci. Kasar Sin ta ba da muhimmiyar gudummowa wajen yaki da ta'addanci a duk fadin duniya. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China