Kana ya ce, a matsayinta ta kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin tana da babban nauyin rage adadin iska mai gurbata muhalli da take fitarwa, haka kuma za ta zuba kudade masu yawa kan wannan aiki.
Kaza lika, ya ba da shawara cewa, ya kamata a dauki matakai yadda ya kamata domin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 13 a nan kasar Sin ta fuskar rage iskar Carbon Dioxide da za a fitar, da dukufa wajen cimma burin rage sama da kashi 45 bisa dari na wannan iska ya zuwa shekarar 2020 idan aka kwatanta da na shekarar 2005.
Bugu da kari, ya ce, ya kamata a ciyar da harkar diflomasiyyar yanayi da hadin gwiwar kasashe masu tasowa kan harkokin sauyin yanayi gaba, sannan a gaggauta fara aikin asusun hadin gwiwar kasashe masu tasowa kan harkokin sauyin yanayi da kasar Sin ta bullo da shi. A sa'i daya kuma, kasashen duniya su shiga a dama su cikin ayyukan warware matsalolin sauyin yanayi cikin himma da kwazo, ta yadda za a bullo da tsarin kyautata yanayin duniya mai aldaci ta yadda kowa da kowa zai ci moriyarta. (Maryam)