A jiya Laraba ce zaunannen wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma firaministan kasar Li Keqiang ya halarci taron tawagar wakilan jama'ar lardin Guangdong a taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na NPC da ke gudana a yanzu haka a birnin Beijing, domin tattauna matakan rage gurbatar iska da tabbatar da samar da guraban ayyukan yi da kuma manoma 'yan kwadago dake birane.
Li Keqiang ya jaddada cewa, ana aiwatar da shirin zurfafa yin gyare-gyare da neman samun bunkasuwa ne domin cimma burin kyautata rayuwar jama'a, ta yadda jama'a za su kara samun kudin shiga da kuma jin dadin zamansu.
A yayin taron NPC na wannan karo, Li Keqiang ya halarci tarurukan tawagogin wakilan jama'ar lardunan Shandong da Fujian da birnin Chongqing, domin tattauna rahoton aiki na gwamnati tare da wakilan. Taron tawagar lardin Guangdong shi ne taro na 4 da Li Keqiang ya halarta a yayin manyan taruruka biyu na kasar Sin na wannan shekarar ta 2016.(Lami)