Yau Asabar 5 ga wata, a yayin dake yin rahoto kan ayyukan gwamnatin kasa ta Sin, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, cikin shekarar 2015 da ta wuce, kasar Sin ta shirya bukukuwan cika shekaru 70 da cimma nasarar yaki da mayakan kasar Japan, bayan kawo karshen yakin duniya na biyu, inda kasar ta sanar da muhimmin matsayinta da kuma babban gudummawar da ta bayar cikin yakin duniya na biyu, haka kuma, lamarin ya nuna aniyar al'ummomin kasar Sin kan kiyaye zaman lafiya da yanayin adalci a nan duniya.
Kaza lika, cikin shekarar da ta wuce, kasar Sin ta sami sakamako da dama ta fuskar harkokin diflomasiyya da kuma bisa fannoni daban daban, a matsayin wata babbar kasa, Sin ta kuma ba da gudummawa mai muhimmanci cikin harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya. (Maryam)