A yayin bikin kaddamar da taron, mambobi fiye da dubu 2 na majalisar za su saurari su kuma tattauna kan rahoton da zaunannen kwamitin majalisar zai gabatar kan ayyukan da ya yi a cikin shekarar da ta gabata, da rahoton kan yadda zaunannen kwamitin majalisar ya daidaita shawarwarin da mambobin suka bayar a yayin taron shekara-shekara na bara.
Babban gidan rediyon jama'a na kasar Sin, CNR da gidan talibijin na kasar Sin, CCTV da gidan rediyon kasar Sin, CRI za su watsa abubuwan dake faruwa game da bikin bude taron da kuma rahoton da shugaban majalisar Yu Zhengsheng zai gabatar a yayin biki kai tsaye, sannan, wasu muhimman shafukan intanet na manyan kafofin yada labaru na kasar Sin za su sanar da duniya game da irin wainar da ake toyawa a bikin kai tsaye. (Sanusi Chen)