in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a bude cibiyar watsa labarun "taron NPC" da "taron CPPCC" a ran 27 ga watan Faburairu
2016-02-01 20:19:43 cri
A yayin da ake shirye-shiryen kaddamar da cikakken zama karo na 4 na babban taron wakilan jama'ar kasar Sin, wato NPC a ran 3 ga watan Maris mai zuwa da cikakken zama karo na 4 na babban taron mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wato CPPCC a ran 5 ga watan Maris mai zuwa, yau Litinin 1 ga watan Fabrairu ofisoshin kula da harkokin yau da kullum na NPC da CPPCC sun sanar da cewa, suna maraba da 'yan jaridu na cikin gida da na waje da su watsa labarun wadannan muhimman taruka biyu.

'Yan jaridu za su iya samun labaru da sauran muhimman bayanai game da wadannan taruka biyu da cibiyar yada labaru za ta rika samarwa cikin lokaci a kan shafuffukansu na intanet na http://www.npc.gov.cn/pc/12_4 da http://www.cppcc.gov.cn. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China