in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a ci gaba da bude kofa ga waje, in ji firaministan Sin
2016-03-05 11:01:31 cri
A yayin da yake bada rahoto kan ayyukan gwamnati a yau Asabar 5 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ce, a shekarar bana, za a ci gaba da raya harkokin bude kofa ga waje, domin cimma moriyar juna bisa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen waje.

Haka kuma, a halin yanzu, ana fuskantar canje-canjen yanayin hadin gwiwa da yin gasa ta fuskar tattalin arziki a tsakanin kasa da kasa, shi ya sa, ya kamata a ci gaba da kyautata harkokin tattalin arziki a kasar yadda ya kamata da kuma tsayawa tsayin daka wajen habaka harkokin bude kofa ga waje, ta yadda za a iya karfafa bunkasuwar tattalin arziki da kuma ayyukan yin kwaskwarima a nan kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China