in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayyana tabbacin samun matsakaicin bunkasuwa a shekara 2016
2016-03-02 19:26:24 cri

Kasar Sin ta bayyana tabbacinta na samun matsakaicin saurin bunkasuwar tattalin arziki a shekarar 2016 da muke ciki, sakamakon muhimman matakan gyare-gyare da mahukuntan kasar ke aiwatarwa. Kakakin taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Wang Guoqing wanda ya bayyana hakan yau yayin taron manema labarai gabanin bude taron majalisar a gobe Alhamis ya ce, duk da yanayin da tattalin arikin duniya ke ciki, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa da kashi 6.9 cikin 100, baya ga matukar ingancin da ya ke da shi.

Bugu da kari, Wang ya ce yadda baki ke gudanar da harkokinsu na kasuwanci a kasar shi ma ya inganta. Kana gwamnati a nata bangare ta himmatu wajen samar da yanayin zuba jari daga ketare da zai dace da dokokin kasa da kasa.

Ya kuma bayyana imanin cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kasancewa wurin da zai ci gaba da janyo hankulan masu sha'awar zuba jari da samun riba a duniya. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China