A gun taron, an bayyana cewa, shirye-shirye da shawarwarin da mambobin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin suka bayar, sun hada da dabarun sassa daban daban, wannan ya sa suka zama muhimmiyar hanyar da gwamnati za ta yi amfani da shi wajen sauron ra'ayin jama'a, da sa ido kan ayyukan da gwamnati ke gudanarwa. Aiwatar da shirye-shirye da shawarwarin zai sa kaimi ga gudanar da ayyukan gwamnati bisa kimiyya, ta yadda jama'a za su kara amincewa da gwamnati.
Nan ba da dadewa ba ne za a gudanar da taruka biyu na shekarar 2016. An gudanar da wannan taro a daidai wannan lokaci ne domin sauraron yadda aka aiwatar da shawarwarin bara, hakan ya bayyana muhimmancin da gwamnatin kasar Sin ta dora kan kara inganta aikin kula da shawarwarin da aka gabatar, tare kuma da bayyana nasarorin da aka samu na ba da shawara kan harkokin siyasa.
Tun bayan da aka gudanar da taruka biyu a bara zuwa yanzu, bisa jagorancin hukumomin majalisar gudanarwa, baki daya an aiwatar da kashi 97.1 cikin dari na shirye-shirye, da kuma kashi 96.5 cikin dari. na shawarwarin da aka gabatar. (Fatima)