Tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin sun samu kyakkyawan dawaumammen ci gaba a shekarar 2015
A cikin rahoton da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayar a yayin bikin kaddamar da taron shekara-shekara karo na 4 na majalisar wakilan jama'ar kasar ta 12 da aka yi a safiyar yau Asabar, ya bayyana cewa, a cikin shekarar da ta gabata, ko da yake kasar Sin ta gamu da dimbin matsaloli da kalubaloli masu tsanani, bisa shugabancin kwamitin tsakiya na JKS dake karkashin jagorancin babban sakatarensa Xi Jinping, al'ummomin kasar Sin sun himmatu wajen kawar da matsaloli da kalubaloli, kuma sun samu ci gaban tattalin arziki da zaman al'ummar kasar ba tare da tangarda ba, abin da ya sa suka cimma burin da aka tsaida a farkon shekarar bara.
Li Keqiang ya kara da cewa, a shekarar da ta gabata, tattalin arzikin kasar yana tafiya kamar yadda ake fata, kuma an samu ci gaba wajen gyara tsarin tattalin arzikin kasar. Bugu da kari, an samu ci gaba wajen samar da sabon makamashi maras gurbata muhalli. Sannan, zaman rayuwar al'ummomin kasa ya kara samun kyautatuwa. Dadin dadawa, wasu ilmomin kimiyya da fasahohin zamani sun isa matsayin koli a duniya. (Sanusi Chen)