Ya kamata a gaggauta raya ayyukan noma na zamani
A yau Asabar 5 ga wata, firaminstan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, ya kamata a gaggauta raya ayyukan noma na zamani a shekarar bana, domin kara kudin shiga na manoman kasar Sin. Haka kuma, ya kamata a ci gaba da kyautata manufofin dake shafar kara bunkasa ayyukan noma, ba da tallafi ga manoma da kuma kara musu kudin shiga , yayin da ake zurfafa kwaskwarima a karkara, da kuma habaka hanyoyin neman aikin yi da na samun karin kudin shiga ga manoman kasar Sin, ta yadda za a iya kyautata inganci na ayyukan noma a kasar. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku