Kakakin ya bayyana cewa, bayan tankar da ke makare da mai ta kife ne, sannan mazauna wurin suka fara kwasar man da ke zuba, daga bisani sai wani mutum ya jefa guntun tabar da yake sha a wurin da motar ta fadi lamarin da ya haddasa motar ta kama da wuta.
Kakakin ya kara da cewa, matsalar fashewar tankar mai hadari ne kawai, ba shi da alaka da rikicin da ke faruwa a kasar Sudan ta kudu.
Kawo yanzu, sakamakon karancin kayayyakin kiwon lafiya a wurin, mutane a kalla 20 wadanda suka ji rauni mai tsanani sosai suna cikin mawuyacin hali, kuma mai yiyuwa ne yawan mutanen da suka mutu sanadiyar hadarin zai ci gaba da karuwa. (Sanusi Chen)