in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Museveni ya yi rinjaye a zaben shugaban kasar Uganda
2016-02-19 21:00:58 cri

Kwamitin zabe mai zaman kansa na kasar Uganda IEC ya gabatar da sakamakon zaben shugaban kasar a zagayen farko a Juma'an nan 19 ga wata cewa, shugaba mai ci Mista Yoweri Museveni ya yi rinjaye cikin zaben da aka yi a ranar Alhamis 18 ga wata.

Shugaban kwamitin IEC Mista Badru Kiggundu ya ce, ya zuwa yanzu, an kidaya yawan kuri'un da aka jefa na kashi 36.58 bisa dari, sakamakon ya nuna cewa mutane da suke goyi bayan Museveni ya kai kashi 62.3 bisa dari, inda dan takararsa Mista Kizza Besigye yake bin shi, wanda ya sami kashi 33.46 bisa dari. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China