MDD ta riga ta shigar da kasar Uganda cikin jerin kasashe guda tara dake bukatar taimakon jin kai na gaggawa, kuma za a yi amfani da taimakon kudin wajen bai wa 'yan gudun hijira dake kasar Uganda kayayyakin zaman rayuwa na yau da kullum, domin biyan bukatunsu na gaggawa.
Ana samun yanayin siyasa na zama karko a kasar Uganda, a halin yanzu, 'yan gudun hijira sama da dubu dari biyar suna zama a wannan kasar, kuma galibi daga cikinsu sun zo daga kasashen Congo(Kinshasa), Sudan ta Kudu, Burundi da kuma Somaliya.
Kaza lika, bisa kididdigar da aka yi, 'yan gudun hijira sama da dubu 110 suka shiga kasar Uganda a shekarar 2015, lamarin da ya sa, kasar ta kasance a matsayi na uku cikin manyan kasashen Afirka wadanda suka fi karbar 'yan gudun hijira, yayin da take a matsayi na takwas cikin kasashen duniya kan wannan batu. (Maryam)