Mista Ouyang Daolin, mai bada shawara kan karkokin tattalin arziki a ofishin jakadancin Sin dake Uganda, ya bayyana a cikin wata hira ta baya bayan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa yana da kyau manoman Uganda su daidaita matsayinsu domin samun alfanu ga wannan bukata ta kayayyakin abinci masu tsabta dake karuwa a kasar Sin. A nan gaba, bukata za ta karu a kasar Sin musammun ma ta kayayyakin abinci mai tsabta kamar ruwa lemo da kayan lambu, in ji mista Ouyang. (Maman Ada)