in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uganda ta kammala janye sojojinta daga kasar Sudan ta Kudu
2015-11-02 09:35:55 cri
Sojojin kasar Uganda, dake jibge a kasar Sudan ta Kudu tun yau da kusan shekaru biyu domin kawo karshen rikici tsakanin bangarori masu gaba da juna, sun kammala janyewarsu a ranar Jumma'a. Laftanal kanal Paddy Ankunda, kakakin rundunar sojojin Uganda, ya bayyana a ranar Asabar cewa runkunin karshe na sojojin Uganda sun dawo gida a ranar Jumma'a da yamma.

"Mun kammala janye wa daga kasar Sudan ta Kudu, mun nuna niyyarmu domin yarjejeniyar zaman lafiya ta Addis Abeba", in ji mista Ankunda.

Uganda ta janye dukkannin sojojinta daga kasar Sudan ta Kudu, kamar yadda yarjejeniyar da aka cimma a cikin watan Augustan da ya gabata ta tanada, da kuma shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Rieck Machar, dake shugaban 'yan tawaye a yanzu suka rattaba hannu kanta. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China