Hukumar zaben kasar ta bayyana cewa, sama da mutane miliyan 15.2 da suka cancanci kada kuri'a ne ake saran za su kada kuri'unsu a wannan zabe.
Shugaban kasar mai ci Yoweri Museveni wanda ke mulkin kasar na tsawon sama da shekaru 30 yana fafatawa da manyan adawa guda biyu Amama Mbabazi, tsohon firaministan kasa da Kizza Besigye na babban jami'yyar adawar ta FDC.
Wannan shi ne karon farko da za a yi amfani da na'ura a zabukan kasar, matakin da ake ganin zai magance magudia zaben.(Ibrahim)