Shugaba Musaveni ya bayyana hakan ne a wajen liyafar murnar cika shekaru 66 da kafa sabuwar kasar Sin da aka yi a ofishin jakadancin Sin dake Kamfala, babban birnin kasar Uganda.
A cikin jawabinsa ya ce kasar Sin tana yin taka tsantsan wajen tsoma baki a harkokin kasashe kuma tana nacewa ga bin ka'idojin MDD na daina yin hakan wanda jawabin shi ke misali da tsoma bakin kasashen yammaci da suke nuna ikonsu a kan kasashen Afrika kan yadda za su tafiyar da mulkinsu.
A nashi jawabin Jakadan kasar Sin a Uganda Zhao Yali ya ce kasar Sa za ta ci gaba da tabbaar da samar da zaman lafiya a duniya kuma komai runtsin da za'a shiga ba za ta rabu ko ta nemi mamaye wadansu ba.
Bikin ya samu halartar manyan jami'an gwamnatin kasar ta Uganda da sauran Jami'an diplomasiya na kasashen dake kasar Uganda. (Fatimah Jibril)