Rahotanni na cewa, tun da misalin karfe 7 na safe agogon wurin ne aka fara kada kuri'u a yawancin sassan kasar , koda ya ke an dan samu jinkiri fara kada kuri'a a Kampala,babban birnin kasar da kuma gundumomin da ke kewaye da shi.
Shugaban hukumar zaben kasar Badru Kiggundu ya ce, an samu jinkiri a wasu sassan birnin Kampala da yankunan da ke makwabtaka da shi ne sakamakon raba kayayyakin zaben a makare.Don haka ya yi kira ga 'yan kasar ta Uganda da su kwantar da hankulansu a lokutan zabe.
A nasa bangaren, babban mai sai do na kungiyar tarayyar Turai(EU) a zzabukan na Uganda Eduard Kukan, ya shaidawa manema labarai cewa, zaben ya gudana cikin lumana a sassan kasar daban-daban.(Ibrahim)